Mahukunta 20:21 - Littafi Mai Tsarki21 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?” Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.” Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.