19 Sa'an nan Isra'ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya.
19 Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya.
Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, ya gabatar da Isra'ilawa kabila kabila, aka ware kabilar Yahuza.
Sai Joshuwa ya tashi da sassafe, firistocin suka ɗauki akwatin Ubangiji.
Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.
Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”
Suka kuwa fita su yi yaƙi da mutanen Biliyaminu, suka jā dāgar yaƙi suna fuskantar Gibeya.