Mahukunta 20:15 - Littafi Mai Tsarki15 A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da shida (26,000). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Mutanen Isra'ila suka tafi inda ake sujada suka yi makoki a gaban Ubangiji har zuwa dare. Suka tambaye shi suka ce, “Mu sāke zuwa domin mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu mutanen Biliyaminu?” Ubangiji ya ce musu, “I, ku tafi.” Saboda haka sai sojojin Isra'ilawa suka ƙarfafa, suka sāke jān dāga a inda suka jā ta dā.