Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 20:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 20:10
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.


Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.


Kada su ƙazantar da kansu da irin waɗannan abubuwa, gama da irin waɗannan abubuwa ne al'umman da Ubangiji yake kora a gabansu suka ƙazantar da kansu.


sai a kai yarinyar a ƙofar gidan mahaifinta, sa'an nan mutanen garin su jajjefe ta da duwatsu har ta mutu, don ta yi aikin wauta cikin Isra'ila, gama ta yi karuwanci a gidan mahaifinta. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


Zai zama kuwa wanda aka same shi da haramtattun abubuwa, za a ƙone shi da wuta, shi da dukan abin da yake da shi, domin ya tā da alkawarin Ubangiji, ya kuma yi abin kunya cikin Isra'ila.’ ”


Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila.


Mutanen Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji ƙaƙƙarfan alkawari a Mizfa cewa, “Ba wani daga cikinmu da zai ba da 'yarsa aure ga mutumin Biliyaminu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ