8 Bawan Ubangiji, Joshuwa ɗan Nun, ya rasu yana da shekara ɗari da goma.
8 Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma.
Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra'ilawa.
Suka binne shi a Timnat-sera a ƙasar tuddai ta Ifraimu, arewa da dutsen Ga'ash, a ƙasar gādonsa.
Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”