Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 2:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Duk da haka ba su kasa kunne ga mahukuntan ba. Suka yi wa Ubangiji ha'inci, suka yi wa waɗansu alloli sujada. Kakanninsu sun bi umarnin Ubangiji amma wannan tsara nan da nan suka bar yin haka ɗin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Duk da haka ba su saurari mahukuntansu ba amma sai suka shiga ha’inci da waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Ba kamar kakanninsu ba, nan da nan suka kauce daga hanyar da kakanninsu suka bi, hanyar biyayya ga umarnan Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 2:17
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,


“Sa'an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’


Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Joshuwa, bayan rasuwarsa kuma suka bauta wa Ubangiji dukan kwanakin dattawan da suka ga dukan manyan ayyukan da Ubangiji ya yi domin Isra'ilawa.


“Ku roƙi uwarku, Gama ita ba matata ba ce, Ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta ta daina karuwancinta, Ta rabu da masu rungumar mamanta.


Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama'arsa, Amma sun fi so su yi masa tawaye, Suna ta nutsawa can cikin zunubi.


Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu, Suka zama marasa aminci ga Allah.


Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu, Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.


Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”


Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”


Amma da kuka ga Nahash Sarkin Ammonawa ya zo don ya yi yaƙi da ku, sai kuka ce mini, ‘Mu dai a yi mana sarki da zai sarauce mu,’ alhali kuwa Ubangiji Allahnku ne Sarkinku.


Isra'ilawa kuwa suka bauta wa Ubangiji a dukan zamanin Joshuwa, da dukan zamanin dattawan da suka wanzu bayansa, waɗanda suka san dukan ayyukan da Ubangiji ya aikata domin Isra'ilawa.


Jama'a suka ce wa Joshuwa, “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.”


Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi.


Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.


Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar’ ”


Ubangiji ya ce, “Mutanen Yahuza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun raina koyarwata sun ƙi bin umarnaina. Allolinsu na ƙarya waɗanda kakanninsu suka bauta wa, Sun sa su su ratse daga hanya.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.


Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.


Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra'ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba'al sujada. Suka yi Ba'al-berit ya zama allahnsu.


A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.


Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ