Mahukunta 19:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka dādi, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |