13 mu ƙara ɗan nisa, mu tafi mu kwana a Gibeya ko a Rama.”
13 Ya kuma ce, “Zo, mu yi ƙoƙari mu kai Gibeya ko Rama mu kwana a ɗaya cikinsu.”
“Ku busa ƙaho cikin Gibeya, Ku busa kakaki cikin Rama, Ku yi gangami cikin Bet-awen, Ku yi rawar yaƙi, ya ku Biliyaminu!
Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu.
Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu.
da Zela, da Elef, da Yebus, wato Urushalima, da Gebeya, da Kiriyat. Birane goma sha huɗu ke nan tare da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon mutanen Biliyaminu bisa ga iyalansu.
Amma maigidansa ya ce masa, “Ba za mu tsaya a birnin da mutane ba Isra'ilawa ba ne. Za mu wuce zuwa Gibeya,
Sai suka wuce, suka yi tafiyarsu. Rana ta faɗi sa'ad da suka kai Gibeya, ta yankin ƙasar Biliyaminu.