Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 18:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Suka ce, “Ku tashi, mu tafi mu fāɗa musu, gama mun ga ƙasar tana da ni'ima ƙwarai. Kada ku zauna ku ɓata lokaci, ku shiga ku mallake ta!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Suka ce, “Ku zo mu yaƙe su! Mun ga ƙasar tana da kyau sosai. Ba za ku yi wani abu ba? Kada ku yi wata-wata, ku je kun mallaki ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 18:9
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”


Sai Joshuwa ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku?


Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”


Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”


Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?”


Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”


Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”


Da mutanen nan biyar suka koma wurin 'yan'uwansu a Zora da Eshtawol, sai 'yan'uwan suka tambaye su labarin tafiyarsu.


Idan kuka je za ku tarar da mutane suna zama a sake. Ƙasar kuwa babba ce, tana da dukan abin da ɗan adam yake bukata.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ