A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.
Mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar Layish, suka ce wa abokan tafiyarsu, “Ko kun san akwai gunkin itace cikin gidajen nan? Akwai kuma gunki na zubi, da kan gida, da falmaran dominsu. Me ya kamata mu yi musu?”