Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna.
Mutanen Gileyad suka hana mutanen Ifraimu hayewa ta mashigan Kogin Urdun. Idan wani mutumin Ifraimu gujajje ya ce, “Ku bar ni in haye.” Sai mutanen Gileyad su tambaye shi, “Kai mutumin Ifraimu ne?” Idan ya ce, “A'a,”