Mahukunta 17:3 - Littafi Mai Tsarki3 Ya mayar wa mahaifiyarsa da azurfar dubu da ɗari (1,100). Mahaifiyarsa ta ce, “Domin kada la'anar ta kama ɗana, ina ba da wannan azurfa ga Ubangiji da zuciya ɗaya. Ana iya sassaƙa gunki a kuma yi na zubi saboda haka zan ba ka ita.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Sa’ad da ya mayar da azurfa dubu ɗaya da ɗari ɗaya na shekel wa mahaifiyarsa, sai ta ce, “Na ba da azurfata ga Ubangiji don ɗana yă sassaƙa sura yă kuma yi zubin gunki. Zan mayar maka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.