Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 16:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Da mutane a ɓoye a cikin ɗaki tare da ita, sai ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Da jin haka sai ya tsintsinke igiyoyin kamar zaren da ya yi kusa da harshen wuta. Saboda haka asirin ƙarfinsa bai tonu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 16:9
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kafin tukunya ta ji zafin wuta, Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.


Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”


Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.


Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba'a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”


Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ