Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 16:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Gidan kuwa yana cike da mutane mata da maza. Shugabannin nan biyar na Filistiyawa suna wurin. Akwai mutum dubu uku mata da maza, a kan benen da suka zo kallon wasan Samson.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 To, haikalin ya cika da mutane maza da mata; dukan shugabannin Filistiyawa kuwa suna a can, a bisan rufin kuwa akwai mutum wajen dubu uku maza da mata suna kallon Samson yana wasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 16:27
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.


Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.


Amma kafin 'yan leƙen asirin ƙasar su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin,


Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar.


Samson kuwa ya ce wa yaron da yake jagoransa, “Bari in taɓa ginshiƙan da suke ɗauke da gidan nan, domin in jingina.”


Sa'an nan Samson ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ya Ubangiji Allah, ka tuna da ni, ina roƙonka, ka ƙarfafa ni sau ɗayan nan kaɗai, don in ɗauki fansa a kan Filistiyawa saboda idona biyu da suka ƙwaƙule mini.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ