Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.
Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”