Mahukunta 16:13 - Littafi Mai Tsarki13 Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.” Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai waɗanda suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Sa’an nan Delila ta ce, “Har yanzu, ka mai da shashasha, kana mai da ni wawiya kana kuma yin mini ƙarya. Ka gaya mini yadda za a daure ka mana.” Ya ce mata, “In kin yi kitson gashin kaina guda bakwai kika ɗaura su da zare kika buga su da akwasha, zan rasa ƙarfi in zama kamar kowa.” Saboda haka yayinda yake barci, sai Delila ta yi kitson gashin kansa guda bakwai ta ɗinka su da zare, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |