Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.
Bayan 'yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki.