Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 14:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin 'yan'uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin 'yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce, “Babu wata karɓaɓɓiyar yarinya a cikin zuriyarku ko cikin dukan mutanenmu ne? Dole ne ka tafi wajen Filistiyawa marasa kaciya ka nemi aure?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “A auro mini ita dai. Ita ta dace da ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 14:3
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.


Ƙishirwa kuwa ta kama shi ƙwarai, sai ya roƙi Ubangiji ya ce, “Kai ne ka yi wannan babbar nasara ta hannun bawanka, yanzu kuwa ko zan mutu da ƙishirwa, har Filistiyawa marasa kaciya su kama ni?”


Kada a ba da labarin a Gat, Ko a titin Ashkelon. Kada ku sa matan Filistiyawa su yi murna, Kada ku sa 'yan matan arna su yi farin ciki.


Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, mu aurar da 'yar'uwarmu ga marasa kaciya, gama wannan abin kunya ne a gare mu.


Abram ya ce wa Lutu, “Kada rashin jituwa ya shiga tsakanina da kai ko tsakanin makiyayanka da nawa, gama mu 'yan'uwa ne.


Ibrahim ya ɗibi tumaki da takarkarai ya bai wa Abimelek, su biyu ɗin kuwa suka yi alkawari.


Sa'ad da ya hauro zuwa gida sai ya faɗa wa iyayensa, ya ce, “Na ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa a Timna, ina so ku auro mini ita.”


Gama idan kun kauce, kun koma da baya, kun haɗa kai da sauran al'umman nan da take tare da ku, har kuka yi aurayya da juna,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ