Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 14:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 14:19
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.


Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.


Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa'ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.


Sa'ad da ya zo Lihai, sai Filistiyawa suka sheƙo a guje suna ihu suka nufo shi. Ruhun Ubangiji ya sauko kansa da iko, sai igiyoyin da suke a ɗaure da shi suka tsintsinke kamar zaren da ya kama wuta.


Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.


A rana ta bakwai, kafin rana ta faɗi, mutanen garin suka ce masa, “Me ya fi zuma zaƙi? Me kuma ya fi zaki ƙarfi?” Ya kuwa ce musu, “Da ba don kun haɗa baki da matata ba, Da ba ku san amsar ka-cici-ka-cicin ɗin nan ba.”


Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.


Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?” Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.


Waɗannan su ne siffofin marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin yin hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ