Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 14:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai ya ce musu, “Daga mai ci, abinci ya fito, Daga kuma mai ƙarfi, zaƙi ya fito.” Ba su iya ba da amsar ba har kwana uku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai ya ce, “Daga mai ci, abinci ya fito; daga mai ƙarfi, abu mai zaki ya fito.” Har kwana uku ba su iya ba da amsa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 14:14
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hankaki kuma suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da maraice. Yakan kuma sha ruwa daga rafin.


Duk da haka kuwa a cikin wannan hali duka, har mun zarce ma a ce mana masu nasara, ta wurin wannan da ya ƙaunace mu.


Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.


Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.


Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.


Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.


Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.


Sa'ad da Yehoshafat da jama'arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna ta kwasar ganimar saboda yawanta.


Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat cewa, “Mutane masu yawan gaske suna zuwa su yi yaƙi da kai daga Edom, da kuma teku, har sun iso Hazazon-tamar,” wato En-gedi.


Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni rigunan lilin talatin da waɗansu rigunan na ado.” Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.”


A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ