Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.
Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.
Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado.
Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata, Ina tattara mur da ƙaro. Ina shan zuma da kakinsa. Ina shan ruwan inabi da madara kuma. Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!