Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 13:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Isra'ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 13:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.


Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai.


Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa.


Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada.


Jama'ar Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji zunubi, wato suka bauta wa gunkin nan mai suna Ba'al.


Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada.


Bayan rasuwar Ehud, Isra'ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji.


Mutumin Habasha zai iya sāke launin fatar jikinsa? Ko kuwa damisa za ta iya sāke dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin nagarta, Ku da kuka saba da yin mugunta.


Me kuma zan ƙara cewa? Ai, lokaci zai ƙure mini a wajen ba da labarin su Gidiyon, da Barak, da Samson, da Yefta, da Dawuda, da Sama'ila, da kuma sauran annabawa,


Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Firaton ta ƙasar Ifraimu a tudun Amalekawa.


Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?” Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”


Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.


Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”


Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra'ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama'ila.


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.


Iyayensa ba su san al'amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra'ilawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ