10 Sa'an nan ya rasu, aka binne shi a Baitalami.
10 Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai.
Bayansa kuma, sai Elon mutumin Zabaluna ya shugabanci Isra'ilawa shekara goma.