Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 12:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Mutanen Efraim suka tattaro mayaƙansu, suka haye zuwa Zafon suka cewa Yefta, “Don me ka tafi ka yaƙi Ammonawa ba ka gayyace mu ba? Za mu ƙone gidanka a kanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 12:1
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.


A duk inda kishi da sonkai suke, a nan hargitsi da kowane irin mugun aiki ma suke.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Na nuna muku ayyuka nagari masu yawa daga wurin Uba, a kan wanne a cikinsu za ku jajjefe ni?”


A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”


Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.


Suna ƙina ko da yake ina ƙaunarsu, Har ina yi musu addu'a.


Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?” Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.


wato matan Isra'ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don 'yar Yefta, mutumin Gileyad.


Amma Yefta ya amsa musu, ya ce, “Ni da mutanena mun yi ta jayayya da Ammonawa, na kira ku don ku cece ni, amma ba ku cece ni daga hannunsu ba.


Sa'ad da Ifraimu ta yi magana, mutane suka yi rawar jiki. An ɗaukaka ta cikin Isra'ila, Amma ta yi laifi ta wurin bauta gunkin nan Ba'al, Ta kuwa mutu.


Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ