5 Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob.
5 dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob.
Jama'ar Isra'ila kuwa suka ce wa Sama'ila, “Su wa suka ce Saul ba zai sarauce mu ba? Ka kawo su, mu kashe su.”
Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.
Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.
Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi.
Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”
Ammonawa suka fita suka ja dāgar yaƙi a ƙofar garin, amma Suriyawan Zoba da na Rehob, da mutanen Ish-tobi da na Ma'aka suka ja tasu dāgar a karkara.
Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma'aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).