4 Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi.
4 Ana nan, sa’ad da Ammonawa suka kai wa Isra’ilawa hari,
Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.
Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa.
Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob.
Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaƙi da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”
Sai Nahash Ba'ammone ya kewaye Yabesh da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh kuwa suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”