Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya, Ubangiji mai sakayya ne, mai hasala. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa. Yana tanada wa maƙiyansa fushi.
Ubangiji ya ce, “Kuna tsammani na kori mutanena Kamar yadda mutum yakan saki mata tasa? To, in haka ne ina takardar kisan auren? Kuna tsammani na sayar da ku cikin bauta Kamar mutumin da ya sayar da 'ya'yansa? A'a, kun tafi bauta ne saboda da zunubanku, Aka tafi da ku saboda da laifofinku.
Ubangiji kuwa ya yarda Yabin Sarkin Kan'ana, wanda yake mulkin Hazor ya ci su da yaƙi. Sisera, wanda yake zaune a Haroshet ta al'ummai, shi ne shugaban sojojin Yabin.
Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawan da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune.