Mahukunta 10:6 - Littafi Mai Tsarki6 Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |