Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.
Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada.
Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawan da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune.