Mahukunta 10:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji.