Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 10:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sa'an nan Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suna cewa, “Mun yi maka zunubi, gama mun bar binka, ya Allahnmu, muka yi wa Ba'al sujada.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 10:10
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.’


Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabarsu.


A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.


A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa cece su daga wahalarsu.


Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.


Ammonawa kuma suka haye Urdun don su yaƙi mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na kabilar Ifraimu. Isra'ilawa kuwa suka matsu ƙwarai.


Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.


Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’


Sa'an nan jama'ar Isra'ila suka yi kuka ga Ubangiji suna neman taimako, gama Yabin yana da karusai ɗari tara na ƙarfe, ya kuma tsananta wa Isra'ilawa, ya mugunta musu shekara ashirin. Isra'ilawa kuwa suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.


Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ