Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 1:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Kabilar Manassa ba su kori waɗanda suke zaune a Bet-sheyan, da Ta'anak, da Dor, da Ibleyam, da Magiddo, da garuruwan da suke kusa da su ba, amma Kan'aniyawa suka yi kanekane cikin ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Amma Manasse ba su kori mutane Bet-Sheyan ko Ta’anak ko Dor ko Ibileyam ko Megiddo tare da ƙauyukansu ba, gama Kan’aniyawa sun dāge su zauna a wannan ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 1:27
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“La'ananne ne shi wanda yake yin aikin Ubangiji da ha'inci, La'ananne ne shi kuma wanda ya hana wa takobinsa jini.


Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.


Sarakuna suka zo, suka yi yaƙi a Ta'anak, A rafin Magiddo. Sarakunan Kan'ana suka yi yaƙi, Amma ba su kwashe azurfa ba.


Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”


Daga cikin rabin kabilar Manassa, aka ba su birane biyu, su ne Ta'anak tare da wuraren kiwo nata, da Bileyam tare da wuraren kiwo nata.


Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.


Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.


Sai mutumin ya tafi ƙasar Hittiyawa, ya gina birni, ya sa masa suna Luz, haka ake kiran birnin har wa yau.


Sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan'aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.


Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.


Amma mutanen Biliyaminu ba su kori Yebusiyawan da suke zaune a Urushalima ba domin haka Yebusiyawa suka yi zamansu tare da mutanen Biliyaminu a Urushalima har wa yau.


Suka ajiye makaman Saul cikin haikalin gumakan nan Ashtarot. Suka ɗaure gawarsa a kan garun Bet-sheyan.


A zamaninsa Fir'auna-neko, Sarkin Masar, ya tafi ya tasar wa Sarkin Assuriya da yaƙi a Kogin Yufiretis. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa'ad da Fir'auna-neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Magiddo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ