Sai Danawa suka zaɓi mutum biyar jarumai daga kabilarsu, suka aike su daga Zora da Eshtawol, su tafi leƙen asirin ƙasar, su bincike ta. Suka kuwa tafi zuwa ƙasar tudu ta Ifraimu, suka sauka a gidan Mika.
Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.
Sai Joshuwa ɗan Nun ya aiki mutum biyu 'yan leƙen asirin ƙasa daga Shittim a asirce, ya ce musu, “Tafi, ku leƙo asirin ƙasar, musamman Yariko.” Suka tafi, suka shiga gidan wata mace, karuwa, sunanta Rahab, a nan suka sauka.