56 Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.
56 Sai shi da almajiransa suka tafi wani ƙauye.
Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya domin yă yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.
Ɓarawo yakan zo ne kawai don sata da kisa da hallakarwa. Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”
“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.
Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.
Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya.
Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.
Yesu ya amsa ya ce, “Ku ƙyale su haka.” Sai ya taɓa kunnen bawan, ya warkar da shi.
Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.
Amma ya juya, ya tsawata musu.
Suna tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka duk inda za ka.”
[Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.]