46 Sai musu ya tashi a tsakaninsu a kan ko wane ne babbansu.
46 Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma
Na yi wa ikkilisiya 'yar wasiƙa, amma shi Diyotarifis wanda yake so ya fi kowa a cikinsu, ya ƙi bin maganarmu.
Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.
Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,
A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.
Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.