Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 9:44 - Littafi Mai Tsarki

44 “Maganar nan fa tă shiga kunnenku! Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

44 “Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 9:44
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”


Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.


Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”


Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.” “Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.


Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”


Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata.


Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.


Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.


domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”


Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


Dawuda kuwa ya ce, “Na shiga uku, gara in faɗa a ikon Ubangiji, gama shi mai rahama ne, da in faɗa a ikon mutum.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, yanzu kun gaskata?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ