Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.
Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.
Ga shi, aljani yakan hau shi, yakan yi ihu ba zato ba tsammani. Aljanin yakan buge shi, jikinsa yana rawa, har bakinsa yana kumfa. Ba ya barinsa sai ya kukkuje shi ƙwarai.