4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.
4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin.
Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.
Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.
Da aka yi mata baftisma tare da jama'ar gidanta, ta roƙe mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.
Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.
Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”