Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 9:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Suka amsa suka ce, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawan dā ne ya tashi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 9:19
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.”


Amma waɗansu kuwa suka ce, “Iliya ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawa.”


Sai ya ce wa barorinsa, “Wannan, ai, Yahaya Maibaftisma ne, shi aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


“Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.


Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”


Da jin maganan nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.”


Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”


A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Wata rana yana addu'a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?”


Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Almasihu na Allah.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ