Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 9:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 9:11
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.


ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.


Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.”


Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi?


yana ta wa'azin Mulkin Allah, da koyar da al'amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.


Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.


Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.


ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.


Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.


Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri, Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.


“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.


To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.


Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.


Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Betsaida.


Da rana ta fara sunkuyawa, sha biyun suka matso, suka ce masa, “Sai ka sallami taron, su shiga ƙauyuka da karkara na kurkusa, su sauka, su nemi abinci, don inda muke ba mutane.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ