Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.
Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.
kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka uban al'ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance.