53 Sai suka yi masa dariyar raini, don sun sani ta mutu.
53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.
Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.
Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.
Yesu ya ce, “Ku kawar da dutsen.” Sai Marta, 'yar'uwar mamacin, ta ce masa, “Ya Ubangiji, ai, yanzu ya yi ɗoyi, don yau kwanansa huɗu ke nan da mutuwa.”
Duk wanda ya gan ni Sai yă maishe ni abin dariya, Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
Na lura da yadda mutane suke yi mini mummunar ba'a.
Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini.
Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”
Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”