Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 8:51 - Littafi Mai Tsarki

51 Da ya isa gidan bai yarda kowa ya shiga tare da shi ba, sai Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da kuma uban yarinyar da uwa tata,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 8:51
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu'a.


Sai ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kuma fara jin wahala gaya, yana damuwa ƙwarai.


Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba, Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.


Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.


Su ne Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas,


Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji.


Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”


Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ