Ai kuwa, an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai maganar da aka yi musu ba ta amfane su da kome ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba.
Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.” Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”
Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”
Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.