Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.
Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
Da matar ta ga ba dama ta ɓuya, sai ta matso tana rawar jiki, ta fāɗi a gabansa, ta bayyana a gaban duk jama'a dalilin da ya sa ta taɓa shi, da kuma yadda ta warke nan take.