Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 8:37 - Littafi Mai Tsarki

37 Dukan mutanen kewayen ƙasar Garasinawa suka roƙi Yesu ya rabu da su, don tsoro mai yawa ya kama su. Sai ya shiga jirgi ya koma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

37 Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 8:37
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan suka zo suka tubar musu, bayan kuma sun fito da su, suka roƙe su su bar garin.


“Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”


Sai suka ci gaba, suka tafi wani ƙauye.


Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”


Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”


Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”


Sai suka fara roƙon Yesu ya bar musu ƙasarsu.


Sai ga duk jama'ar garin sun firfito su taryi Yesu. Da suka gan shi, sai suka roƙe shi ya bar musu ƙasarsu.


Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”


Mutanen Bet-shemesh suka ce, “Wa ya isa ya tsaya a gaban Ubangiji, Allahn nan mai tsarki? A wurin wa zai tafi don ya rabu da mu?”


Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.


Waɗanda aka yi abin a idonsu kuwa, suka gaya musu yadda aka warkar da mai aljannun nan.


Mutumin da aljannun suka rabu da shi kuwa, ya roƙe shi izinin tafiya tare da shi. Amma ya sallame shi ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ