Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.
Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”