Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 8:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 8:10
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”


Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,


A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.


‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.’ ”


Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.


Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,


Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.


“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”


Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”


“Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.


don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ