50 Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”
50 Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”
Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”
Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
Yesu ya ce masa, “Karɓi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.
Sai Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan take ya gani, ya bi Yesu, suka tafi.
Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi, Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.
Yana da 'ya ɗaya tilo, mai shekara misalin goma sha biyu, tana kuma bakin mutuwa. Yana tafiya, taro masu yawa na matsa tasa,
Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”
Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.
Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.”
Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”
Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”