Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 7:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Yesu ya amsa ya ce, “Saminu, ina da magana da kai.” Sai shi kuma ya ce, “Malam, sai ka faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 7:40
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu ne muka tabbata ka san kome, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”


Yesu kuwa ya sani suna so su tambaye shi, sai ya ce musu, “Wato kuna tambayar juna ne abin da nake nufi da cewa, ‘Bayan ɗan lokaci kaɗan ba za ku gan ni ba, bayan ɗan lokaci kaɗan kuma za ku gan ni’?


Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.


Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”


Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”


Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.


Da Yesu ya gane wuswasinsu, ya amsa musu ya ce, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’


Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.


Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’


To, da Bafarisiyen da ya kira shi ya ga haka, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce, da kuma ko wace irin mace ce wannan da yake taɓa shi, don mai zunubi ce.”


Yesu ya ce, “Wani yana bin mutum biyu bashi, ɗaya dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.


Sa'an nan ya ce, “Ina da wani abin da zan faɗa miki.” Ta ce, “To, sai ka faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ